Insane
Darus-sahaba
1jojlxKOMkX9WyteRe4hGfd...5Tlzwos6Wa8pU99NjJEjmoO7lE72qs...P8zLBUI5VEdw01bf9Bj3WN2UJZQ0kMkumqAOI9CU319yy4DVw
Maraba Da Zuwa Wannan
Shafi Mai Al-barka

wanna shafi yana zuwa muku kai tsaye daga masallacin jumu'a
Jami'u Abu hurairah
Dake kurna y'an kifi titin y'an smogal a karamar hukumar dala dake kano Nigeria
kar kashin jagorancin
Sheik Muhammad Sani Uthman Kurna

Home
Karatut-tukan Sheik Muhammad Thani Uthman Kurna
Mata A Musulunci
Bayanin Zakka
Bayanin Azumi
Bayanin Hajji da Umara
Kasuwanci mai ribar gaske
Muhimmin Sako Zuwa ga Ma'aurata
Tsarin Mu'amala A cikin Musulunci
Hakkokin Manzon Allah s a w Akan Alumarsa
Shin hadin kai zai yiwu tsakanin Ahalussunnah da shi a
Wadanna mata aka Haram tawa musulmi da kuma wanda aka Halarta
Hukunce - Hukunce da suka shafi mata
Jinin Al ada ga mata
Jagoran mai wa azi
Adduo in manzon Allah s a w
Falalar Karatun Al-kur'ani
Falalar Sahabbai {R.A}
Falalar Sahabbai {R.A} Daga bakin Imamai
Tarihi
Falalar Ahlulbait daga bakin Ahlussunnah
Tambayoyi masu muhimmanci A cikin Addinin Musulunci
Ayyukan Zuci
Tattaunawa Ta Nitsuwa
Addinin Shi'a
Hukunce-Hukuncen Da Suka Shafi Mata
Karatut-tukan Malamai da Lakcocin su



2014-10-13

-----------------------------------
Tags: Abdulmajid

SALON DA ,AWA.

Gabatarwa Yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah. Tsira da aminci su tabbata ga fiyayyen halitta, Manzon Allah, da alayensa da sahabbansa da waxanda suka bi tafarkinsu zuwa ga ranar sakamako. Bayan haka : Babu ko shakka kira zuwa ga addinin Allah yana xaya daga cikin manya-manyan wajiban addini, domin ta hanyarsa ne a gane qarya da gaskiya, shiriya da vata, daidai da ba daidai ba, don haka ma Allah Maxaukakin Sarki ya aiko da Manzanni da Annabawa don su koyar da mutane, su kira su zuwa ga addinin gaskiya. Allah Maxaukakin Sarki yana cewa : Ma'ana : "Haqiqa Mun aiko da Manzanninmu da hujjoji, kuma mun saukar musu da littattafai da mizani don mutane su tsaya a kan gaskiya" (Alhadid : 25). Don haka kiran mutane zuwa ga addini da karantar da su, da yi musu wa'azi aiki ne na Annabawan Allah da Manzanni. Mahimmancin Da'awa A Musulunci Aikin da'awa ba qaramin mahimmanci ne da shi ba a addinin musulunci, aiki ne mai gwaggwavan lada a wurin Allah Maxaukakin Sarki. Allah (S.W.T) yana cewa : ﭽ ﭼ ﭽ ﭾ ﭿ ﮀ ﮁ ﮂ ﮃ ﮄ ﮅ ﮆ ﮇ ﮈ ﮉ ﭼ فصلت: ٣٣ Ma'ana : "Waye yafi kyakkyawan zance fiye da wanda ya yi kira zuwa ga Allah, ya yi aiki nagari ya kuma ce ni ina cikin musulmi" (Fussilat : 33). A cikin wannan aya zamu ga Allah Mai girma da buwaya yana yabon masu da'awa da aiki nagari, da cewa babu wanda ya fi su kyan zance da magana. Sheikh Abdul-Aziz bin Baz – Allah ya yi masa rahama – yana cewa : "Ma'anar ayar ita ce, babu wanda ya fi shi (wato mai kira zuwa ga Allah) kyakkyawar magana, saboda ya yi kira zuwa ga Allah, ya yi nuni zuwa gare Shi, kuma ya yi aiki da abin da ya yi kira zuwa gare shi. Ma'ana ya yi kira zuwa ga gaskiya kuma ya yi aiki da ita, ya yi inkarin varna kuma ya tsoratar daga gare ta, kuma duk da haka bai ji kunya ba, ya bayyana abin da yake kai ya ce, "Ni ina cikin masulmi"(). A wani wurin Allah Maxaukakin Sarki yana cewa Annabinsa (S.A.W) : ﭽ ﮀ ﮁ ﮂ ﮃ ﮄ ﮅﮆ ﮇ ﮈ ﮉ ﮊ ﮋﮌ ﮍ ﮎ ﮏ ﮐ ﮑ ﮒ ﮓ ﭼ [يوسف: ١٠٨] Ma'ana : "Ka ce wannan shi ne tafarkina, ina kira zuwa ga Allah a kan hujja (basira) ni da duk wanda ya bi ni. Tsarki ya tabbata ga Allah, ba na cikin masu tarayya da Allah". (Yusuf : 108). A cikin wannan ayar zamu ga Allah Maxaukakin sarki yana bamu labarin cewa haryar Manzon Allah (S.A.W) da muminan da suka bi shi, ita ce kira zuwa ga Allah, kira zuwa ga kaxaita Allah (S.W.T) a cikin bauta, a bisa hujja da basira. Haka kuma hadisi ya tabbata a cikin "Sahihu Muslm" daga Abu Hurairata Allah ya yarda da shi, ya ce, Manzon Allah (S.A.W) ya ce, «مَنْ دَعَا إِلَى هُدًى، كَانَ لَهُ مِنَ الأَجْرِ مِثْلُ أُجُورِ مَنْ تَبِعَهُ، لاَ يَنْقُصُ ذَلِكَ مِنْ أُجُورِهِمْ شَيْئًا. وَمَنْ دَعَا إِلَى ضَلاَلَةٍ كَانَ عَلَيْهِ مِنَ الإِثْمِ مِثْلُ آثَامِ مَنْ تَبِعَهُ، لاَ يَنْقُصُ ذَلِكَ مِنْ آثَامِهِمْ شَيْئًا» رواه مسلم. Ma'ana : ((Duk wanda ya yi kira zuwa ga shiriya, to yana da lada kwatankwacin ladan waxanda suka bi shi, kuma hakan bai tauye musu komai daga cikin ladansu ba. Hakanan duk wanda ya yi kira zuwa ga vata, to yana zunubi kwatankwacin zunuban waxanda suka bi shi, kuma hakan bai tauye musu komai daga zunubansu ba". Muslim ne ya rawaito shi. Idan muka dubi wannan hadisi zamu ga cewa mai da'awa zuwa ga addini yana da ximbin lada, wanda Allah Maxaukakin Sarki ne kaxai ya san iya adadinsa, domin kuwa babu wanda ya san iya waxanda suke amfanuwa da da'awar mai da'awa sai Allah. A wani hadisin da Imam Muslim ya rawaito daga Abdullahi xan Mas'ud – Allah ya qara masa yarda – ya ce, Manzon Allah (S.A.W) ya ce : ((من دل على خير فله مثل أجر فاعله)) رواه مسلم. Ma'ana : ((Wanda ya yi nuni zuwa (aikin) alheri, to yana da kwatankwacin ladan wanda ya aikata (alherin). Muslim ne ya rawaito shi. Lamarin da'awa bai tsaya nan ba, saboda ya tabbata a hadisi, Manzon Allah (S.A.W) ya ce wa Aliyyu xan Abi Xalib – Allah ya qara masa yarda - : ((فَوَاللَّهِ لأَنْ يَهْدِيَ اللَّهُ بِكَ رَجُلاً خَيْرٌ لَكَ مِنْ أَنْ يَكُونَ لَكَ حُمْرُ النَّعَمِ)). Ma'ana : "Wallahi, Allah ya shiryi mutum xaya da kai, ya fi a ce kana da jajayen dabbobi". Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi. Saboda Mahimmancin wannan aiki na da'awa Manzon Allah (S.A.W) yake aika sahabbansa zuwa ga wasu garuruwa don kiran mutane da ilmantar da su, kamar yadda ya aiki Mu'azu xan Jabal da Aliyyu xan Abi Xalib zuwa Yemen, ya aika Mus'ab xan Umair zuwa ga Madinah kafin ya yi hijira, ya aika mutum saba'in daga sahabbansa zuwa ga wasu mutane don su karantar da su Alqur'ani da Sunnah, da dai sauransu, duk wannan yana nuna mana mahimmancin da'awa, kuma babu yadda za a yi al'umma ta rayu kyakkyawar rayuwa sai da masu da'awa zuwa ga gaskiya, zuwa ga ingantaccen addini, in kuwa aka rasa to wannan al'ummar ta lalace, don haka buqatar al'umma zuwa ga masu da'awa ta gaskiya, waxanda za su xora al'umma a kan addini ingantacce, tafi buqatar al'ummar zuwa ga abinci da abin sha, saboda qarshen wanda ya rasa abinci shi ne mutuwa, amma zai iya mutuwa ya shiga Aljannah, savanin wanda yake kan vata da shirka da kafirci qarshensa idan bai samu mai tsamo shi ba, shi ne halaka da tavewa duniya da lahira. Allah ya kiyaye mu. Kashe-Kashen Waxanda Ake Wa Da'awa Waxanda ake yi wa da'awa sun kasu gida-gida, kuma yana da matuqar mahimmanci ga mai da'awa ya sansu, don ya san ina ne yake fuskantar da da'awarsa, kuma wane salo ya kamata ya bi a wajen da'awar, saboda haka malamai sun kasa waxanda ake wa da'awa zuwa gida biyu, a kuma qarqashin kowanne kaso akwai wasu kashe-kashen, ga su kamar haka : Kashi Na Farko : Musulmai, waxanda suka yi imani da Allah, suka amsa saqon da Manzon Allah (S.A.W) ya zo da shi. Waxannan su ne waxanda malamai suke ce musu "Ummatul Ijaba" sun kuma kasu zuwa gida uku : • Waxanda suka yi gaba a cikin ayyukan alheri (Sabiquuna Bil Khairati). Su ne waxanda suke yin nafilfili a kan ayyukan wajibai da Allah ya xora musu. • Waxanda suke tsaka-tsakiya (Muqtasiduuna). Su ne waxanda suka tsaya a kan wajibai. • Waxanda suka zalunci kansu (Zalimiy Anfusihim) Su ne musulmai masu savo. Waxannan su ne kashe-kashen na farko, Allah ya faxe su a cikin suratul Faxir aya ta 32. Wannan kaso ana yi musu da'awa ne zuwa ga tabbata a kan addinin da barin abin da ya sava masa. Kashi Na Biyu : Kafirai Waxanda ba musulmai ba. Su kuma sun kasu da yawa, amma zamu iya haxe su a cikin waxannan kashe-kashen masu zuwa : 1. Masu inkarin samuwar Allah da ayyukansa (Malahidah). 2. Masu haxa Allah da wani wajen bauta (Al-Mushrikuuna). 3. Waxanda suka yi ridda suka bar addinin musulunci. 4. Ma'abota Littafi, kamar Yahudu da Nasara (Ahlul Kitab). 5. Munafikai, waxanda suka bayyana addini a baki, suka voye kafirci a zuci. Waxannan sune kashe-kashen waxanda ba musulmi ba, kuma dukkaninsu suna buqatar da'awa. Don haka wajibi ne akan mai da'awa ya san salo da hanyar da zai fuskanci kowanne kaso daga cikin waxannan, domin salon da ya dace da mai inkarin samuwar Allah ba lallai ba ne ya dace da wanda yake ahlul kitabi kirista ko bayahude, kamar yadda salon da ya dace da musulmi mai savo ba lallai ba ne ya dace da kafiri ba, saboda haka yana da kyau mai da'awa ya san da su wa yake mu'amala, kuma ta yaya zai kira su. Matakan Da'awa Duba Da Yanayin Waxanda Ake Wa Da'awar Kasancewar waxanda ake wa da'awa sun kasu gida-gida to ya zama wajibi a samu matakai daban-daban wajen yin da'awar, don da'awar ta yi daidai da kowanne vangare. Malamai sun dunqule matakan da'awa – duba da waxanda ake wa da'awar – zuwa gida uku, su ne : Hikima, kyakkyawan wa'azi, da kyakkyawar jayayya (Mujadala). Allah Maxaukakin Sarki ya faxi waxannan matakai a cikin faxinsa : ﭽﮦ ﮧ ﮨ ﮩ ﮪ ﮫ ﮬﮭ ﮮ ﮯ ﮰ ﮱﯓ ﯔ ﯕ ﯖ ﯗ ﯘ ﯙ ﯚ ﯛﯜ ﯝ ﯞ ﯟ ﯠ ﭼ [النحل: ١٢٥]. Ma'ana : "Ka yi kira zuwa ga tafarkin Ubangijinka da hikima da wa'azi kyakkyawa. Ka yi jayayya da su ta hanyar da ta fi kyau. Haqiqa Ubangijinka shi ne masanin wanda ya vace daga tafarkinsa, kuma shi ne ya san shiryayyu". (Annahal : 125). Ibnul Qayyim – Allah ya yi masa rahama – yana cewa wajen fassara wannan ayar : "Sai Allah (S.W.T) ya ambaci matakan da'awa, ya sanya su kashi uku, gwargwadon halin waxanda ake wa da'awar, saboda kodai (wanda ake wa da'awar) ya kasance mai neman gaskiya ne, mai kwaxayinta, da son ta, da gabatar da ita akan abin da ba ita ba, to wannan za a yi masa da'awa da hikima ne, ba ya buqatar wa'azi ko jayayya. Ko kuma wanda ake wa da'awar ya kasance ya bijire ya shagala da abin da ba gaskiya ba, amma idan aka nuna masa gaskiyar zai gane ta, ya bi ta, ya fifita a kan waninta, to wannan yana buqatar hikima da wa'azi na tsoratarwa da kwaxaitarwa. Ko kuma ya kasance mai taurin kai da bijirewa, to wannan za a yi masa da'awa da jayayya mai kyau" (Duba Assawa'iqil Mursala : 4/1276 – 1277). A taqaice dai, idan muka dubi wannan aya zamu ga cewa duk wani matakin wa'azi da za a yi, ba zai fita daga xayan ukun nan ba. Hanyoyin Kiran Kafirai Zuwa Musulunci Duba da cewa mafi yawancin waxanda suke nan, masu wa'azin maguzawa ne, zamu xauki hanyoyin da ake bi wajen kiran waxanda ba musulmi ba (Kafirai) mu yi bayani a kansu. Babbar hanyar farko wajen kiran kafirai zuwa ga musulunci ita ce hanyar da Alqur'ani ya bi, wadda take qunshe da hujjoji da dalilai gamsassu, waxanda sun isa su jawo duk wanda Allah ya yi masa gamon-katar zuwa ga rungumar addinin musulunci. Idan muka dubi Alqur'ani zamu iya dunqule hanyoyin kiran kafirai zuwa ga addinin musulunci cikin hanyoyi masu zuwa : 1 – Hanya Ta Farko : Bayanin kyan addinin musulunci, ta hanyar faxin kyawawan abubuwan da ya qunsa, na gaskiya, amana, haquri, girmama na gaba, tausaya wa na qasa, baiwa duk mai haqqi haqqinsa, da sauransu. A nan wajibi ne mai da'awa ya zama yana nuna waxannan halaye a aikace, fiye da faxi da baki. 2 – Hanya Ta Biyu : Qoqarin warware musu abubuwan da aka faxa musu game da addini, wanda ba daidai ba, da hujjoji na nassi da hankali. 3 – Hanya Ta Uku : Tunatar da su qarshen al'ummun da suka gabata, da irin yadda Allah ya halakar da su yayin da suka qi gaskiya. Anan yana da kyau mai da'awa ya yi qoqarin haxa abubuwan da suke faruwa na musibu a yau da savawa Allah da ake yi, kamar abin da ya faru na
Back to posts
This post has no comments - be the first one!

UNDER MAINTENANCE


........................................................
TSARIN LOKUTAN KARATUT-TUKAN MU
TSARA-TSARAN KARATUTTUKAN DA AKE GABATARWA A MAJALISIN DARUS SAHABA,DAKE GOBIRAWA TITIN YAN SUMOGAL.
1.TAHFIZUL QUR'AN.
Daga ranar Asabar zuwa Laraba.
Daga karfe 7:30 na safe zuwa 5:00 na yamma

2.KARATUN MAZA MANYA.
Daga ranar litinin zuwa alhamis, daga karfe 8:00 na dare zuwa karfe 10:00 na dare.
3.KARATUN MATAN AURE.
Ranar alhamis da juma'a daga karfe 2:30 na yamma zuwa 5:00 na yamma.
JERIN KARATUTTUKAN DA SHUGABAN MAJALISIN YAKE GABATARWA A KWANUKAN CIKIN SATI.
1.KARATUN ZAURE
DAGA SAllar asubah zuwa karfe 9:00 na safe a kowacce rana,banda Alhamis da juma'a
2.KARATUN BULUGUL MARARM
A MASAllacin malam bakao dake kurna yan kifi,ranar alhamis magribah zuwa ish'sha
3.KARATUN JAMI'U MUTUNIN TAUHEED WAL AQIDAH.
Ranar lahadi shi ma a masallacin malam bako,magribah zuwa ish'sha.
4.KARATUN MANHAJIL MUSULUM,
MASALLACIN JUMA'A NA ABU HURAIRAH Dake gobirawa yan sumogal,ranar laraba magribah zuwa ish'sha.
5.KARATUN AHKAMUL JANA'IZ
,A MASALLACIN UMAR BIN KATTAB R.A,
Dake dan dinshe kusa da filin dantata,magriba zuwa ish'sha.
Ranar talata

6.KARATUN MATA NA LITTAFIN MANZUMATUL HA'IYYA
A kowacce lahadi daga 9:30 na safe zuwa 11:30 na safe,a masallacin Abu hurairah
7.KARATUN MATA NA LITTAFIN ZADIZ ZAUJAINI
Shi ma a masallacin abu hurairah,a kowacce Asabar daga karfe 9:30
na safe zuwa 11:30 na sa fe.

8.KARATUN TAFSIRI
A DUK RANAR LAHADI Asubah zuwa karfe 8:00 na safe.
...........................................................


Shafuka masu Alaka da mu
Basheer journalist sharfadi





Kuna iya tuntu6ar mu ta wadannan hanyoyin
Abdul-majid Ibn Nuh ta face book

KO TA SHAFIN MU NA FALALAR SAHABBAI DAGA BAKIN IMAMAI TA FACE BOOK.

Ko ta watsAp A 07063276717
Bugo mana waya ta nan
Bugo mana waya ta nan
Bugo mana waya ta nan
Ko ta Email A

Home


Copyright © 2014 - 2015By:- Abul-majid Ibn Nuoh Powered by- Basheer journalist sharfadi