IMANI DA RASSAN SA GUDA 67 NAWA KAKE DA SU A CIKI.?
IMANI DA RASSAN SA GUDA 67, NAWA KAKE DA SU A CIKI.?
Manzon Allah saw yace: Imani yana da rassa guda Sitttin bakwai , ko sabain da bakwai, mafi daraja, shine ,Lailaha illalahu, mafi karanta dauke abu mai cutarwa daga hanya, kunya tana daga cikin imani. Muslum ya ruwaito
Malamai sunyi bincike domin gano wadannan rassa, sun wallafa littafai da dama akan haka, abinda suka kawo, daga Alkur'ani mai girma, da ingatattun hadisai, kuma sun gaya mana cewa wadannan rassa sun fito daga aiyukan zuciya, da aiyukan harshe, da aiyukan gabbai, kuma imani yana karuwa yana raguwa.
1- Imani da Allah, shi yayi halitta, shi ya mallaka. shi yake gudanarwa.shi ya cancanci bauta. Da sunayansa da siffofinsa.
2- Imani da Mala'ikun Allah, da siffofin su da aiyukan su, da sunayansu.
3- Imani Da Manzannin Allah swt.
4- Imani da littafan Allah swt,
5- Imani da ranar Lahira.
6- Imani da kaddara mai dadi da mara dadi.
7- Imani da tashi bayan mutuwa
8- Imani da tattaruwa a gaban Allah domin hisabi
9- Imani da Aljannah da Wuta.
10- Kaunar Allah,
11- Tsoran Azabar Allah
12- Kauna juna da Fatan samun rahmar Allah
13- Wajabcin dogaro ga Allah
14- Wajancin Kaunar Manzon Allah saw.
15- Wajabcin girmama Manzon Allah saw.
16- kula da addinin sa da kishinsa.
17- Wajabcin Neman Ilmi.
18- Yada ilmi da koyarwa.
19- Girmama Alkur'ani karatunsa, fassararsa, aiki dashi
20 -wajabcin yin tsarki,na wanka da alwala da taimama.
21- Kula da salloli,biyar akan lokaci.
22- Fitar da zakka, ga wadanda suka cancanta.
23- Azumin Ramadan.
24- Shiga i'itikafi, sunnah ne, yana kara imani
25- Aikin Hajji, sau daya wajibi, komawa sunnah.
26- Jihadin kare addini da yadashi, bisa ilmi.
27- Rashin gudu daga filin daga idan ana yaki.
28 - Bayar da daya bisa biyar, ga abinda mutum ya samu na Rikazi, wato ( tono kudi a kasa)
29- Fitar da kaffara idan ta hau kan mutum, na kisa ko rantsuwa, ko zihari, ko karya azumi da gangan
30- Cikawa da Alkawari idan an dauka.
31- Rikon Amana
32- Godiya ga ni'imar Allah da rashin butulci.
33- Kiyaye harshe, fadin alkhairi ko shiru
34- Tsare kafofin musulunci, kamar (media) wanda ya taba addini a mayar masa da martani.
35- kada mutum ya kashe kansa. Ta ko wacce hanya
36- kamai mutunci,
37- Nisantar cin Haram
38- Tuba daga laifuffuka.
39 Bin sunnah sau da kafa da zuciya
40- Yin aiki da lklasi (ayi aiki don Allah kawai)
41- Hakuri, da rashin zalama
42 - Tausayi da jin kai
43- Tawali'u da kan-kan da kai
44- Zuhdu, gudun duniya, da abin hannun mutane
45- Girmama Manya da tausayawa na kasa.
46- Yawan Addua
47, Yawan Zikri
48, yawan salati ga Annabi saw.
49, Yawan Kyauta da alkhairi
50, Yawan Istigfari
51, sada zumunta
52, Biyayya ga iyaye.
53, Tarbiyyar y'ay'a
54, Kula da hakkin iyali.
55, Biyyaya ga na gaba cikin bin Allah.
56, Tsayar da adalci, ga masoyi da makiyi
57, Yin Sulhu tsakanin Jamaa
58, Umarni da kyakyawa da hani da mummuna
59, Yin Gaskiya
60, Neman kudi ta hanyar halal
61, Yin sallama da amsa sallama
62, Bayan da rancan kudi babu ruwa
63, Girmama bako
64, Amsawa mai atshawa
65, Taimakekiniya wajan aikin alkhairi.
66, Dauke abinda zai cuci mutane daga hanya.
67, ka fifita dan uwanka akanka ko kana da bukata.
Allah ya bamu ikon aikatawa.
Created at 2014-11-09 21:01:43
Back to posts
UNDER MAINTENANCE
Allah ya saka
Allahu-AKKBAR