Disneyland 1972 Love the old s
Darus-sahaba
1jojlxKOMkX9WyteRe4hGfd...5Tlzwos6Wa8pU99NjJEjmoO7lE72qs...P8zLBUI5VEdw01bf9Bj3WN2UJZQ0kMkumqAOI9CU319yy4DVw
Maraba Da Zuwa Wannan
Shafi Mai Al-barka

wanna shafi yana zuwa muku kai tsaye daga masallacin jumu'a
Jami'u Abu hurairah
Dake kurna y'an kifi titin y'an smogal a karamar hukumar dala dake kano Nigeria
kar kashin jagorancin
Sheik Muhammad Sani Uthman Kurna

Home
Karatut-tukan Sheik Muhammad Thani Uthman Kurna
Mata A Musulunci
Bayanin Zakka
Bayanin Azumi
Bayanin Hajji da Umara
Kasuwanci mai ribar gaske
Muhimmin Sako Zuwa ga Ma'aurata
Tsarin Mu'amala A cikin Musulunci
Hakkokin Manzon Allah s a w Akan Alumarsa
Shin hadin kai zai yiwu tsakanin Ahalussunnah da shi a
Wadanna mata aka Haram tawa musulmi da kuma wanda aka Halarta
Hukunce - Hukunce da suka shafi mata
Jinin Al ada ga mata
Jagoran mai wa azi
Adduo in manzon Allah s a w
Falalar Karatun Al-kur'ani
Falalar Sahabbai {R.A}
Falalar Sahabbai {R.A} Daga bakin Imamai
Tarihi
Falalar Ahlulbait daga bakin Ahlussunnah
Tambayoyi masu muhimmanci A cikin Addinin Musulunci
Ayyukan Zuci
Tattaunawa Ta Nitsuwa
Addinin Shi'a
Hukunce-Hukuncen Da Suka Shafi Mata
Karatut-tukan Malamai da Lakcocin su



2014-10-13

-----------------------------------

MANYAN LAIFIKA GUDA 70 NA WA KAKE AYKATAWA.

MANYAN LAIFUFFUKA 70 NAWA KAKE AIKATAWA DAGA CIKI ?

Manyan malamai sunyi kokarin tattara, manyan laifukkuka, a guri guda domin sanin su, da fahimtar munin su, da yadda zaa guje musu.
Allah ya bamu ikon kiyayewa.

1- Shirka da kashe-kashenta
2- kisan kai
3 - Tsafi
4- Wasa da sallah
5- Hana zakka
6- Sabawa iyaye
7- Cin riba
8- Cin dukiyar marayu
9- yiwa Annabi saw karya
10- Karya Azumi da gangan
11- Gudu daga filin daga ana yakin kare addini.
12- Yin Zina
13- Shugaba mai hainci ga talakawansa.
14- Shan giya da sarrafata
15- Girman kai da takama da jiji da kai
16- Shedar Zur
17- Luwadi da mdigo
18- Yin kage ga muminai
19- Satar dukiya daga baitul mali
20- Zaluncin cin dukiyar jamaa, ta algus da manuba.
21- Sata, da sane.
22- Fashi da makami
23- Rantsuwar karya
24- Yawan karya
25- Wanda ya kashe kansa da gangan
26- Mugun Alkali,
27- Maza masu koyi da mata da Mata masu koyi da maza
28- Masu auran kisan wuta
29- Masu cin mushe da shan jini da alhanzir
30- Rashin tsarki daga fitsari.
31- Masu karbar dukiyar Jamaa babu dalili
32- Munafinci
33- Ha'inci
34- Yin ilmi don duniya da boye ilimi mai amfani
35- Yin gori idan ka yiwa mutum wani alkhairi,.
36- Karyata kaddara
37- magulmaci
38- Mai yawan laantar mutane
39- mayaudari
40- Gasgata bokaye da yan tsibbu
41- Mace mai tsiwa ga mijinta
42- Rashin sada zumunta
43- Sassaka gumaka
44- Annamimanci
45- Kukan mutuwa (yin hawaye babu laifi)
46- Sukan Nasabar mutane, da cin mutunci.
47- Cutar Jamaa, ta kowacce fuska.
48- Kafurta mutane,babu dalilin daga sharia
49- Dunguma ashariya da yawan zage- zage.
50- Zagin waliyai da bayin Allah malamai
51- Jan tufafi a kasa,
52- Sanya tufafin alhariri,
53- Yanka dabba da sunan wani. ba Allah ba.
54- Wanda ya shiga iyakar kasar wani, ko gonar sa ko filinsa.
55- Zagin sahabbai.
56- Mace mai karin gashi.da zane, da yin wushirya da aske gashin gira.
57- Kiran Mutane zuwa ga bata, ko koyar da barna.
58- Wanda yake yiwa dan uwansa barazana da makami.
59- Mai daukan rahoton musulmi yana kaiwa makiyansu.
60- Tauye mudu
61- Jayyaya da musu mara amfani a cikin addini
62- Mutumin da baya jingina kansa ga iyayansa.
63- fidda tsammani daga Rahmar Allah.
64- Camfi
65 - Shan ruwa ko abinci a kofin zinarai.
66- Gaba da juna
67- Butulci
68, Caca
69- Keta alfarmar haramin Macca da Madina.
70 - Cin Zarfin makoci.
ALLAH YA TSARE MU.

Back to posts
This post has no comments - be the first one!

UNDER MAINTENANCE


........................................................
TSARIN LOKUTAN KARATUT-TUKAN MU
TSARA-TSARAN KARATUTTUKAN DA AKE GABATARWA A MAJALISIN DARUS SAHABA,DAKE GOBIRAWA TITIN YAN SUMOGAL.
1.TAHFIZUL QUR'AN.
Daga ranar Asabar zuwa Laraba.
Daga karfe 7:30 na safe zuwa 5:00 na yamma

2.KARATUN MAZA MANYA.
Daga ranar litinin zuwa alhamis, daga karfe 8:00 na dare zuwa karfe 10:00 na dare.
3.KARATUN MATAN AURE.
Ranar alhamis da juma'a daga karfe 2:30 na yamma zuwa 5:00 na yamma.
JERIN KARATUTTUKAN DA SHUGABAN MAJALISIN YAKE GABATARWA A KWANUKAN CIKIN SATI.
1.KARATUN ZAURE
DAGA SAllar asubah zuwa karfe 9:00 na safe a kowacce rana,banda Alhamis da juma'a
2.KARATUN BULUGUL MARARM
A MASAllacin malam bakao dake kurna yan kifi,ranar alhamis magribah zuwa ish'sha
3.KARATUN JAMI'U MUTUNIN TAUHEED WAL AQIDAH.
Ranar lahadi shi ma a masallacin malam bako,magribah zuwa ish'sha.
4.KARATUN MANHAJIL MUSULUM,
MASALLACIN JUMA'A NA ABU HURAIRAH Dake gobirawa yan sumogal,ranar laraba magribah zuwa ish'sha.
5.KARATUN AHKAMUL JANA'IZ
,A MASALLACIN UMAR BIN KATTAB R.A,
Dake dan dinshe kusa da filin dantata,magriba zuwa ish'sha.
Ranar talata

6.KARATUN MATA NA LITTAFIN MANZUMATUL HA'IYYA
A kowacce lahadi daga 9:30 na safe zuwa 11:30 na safe,a masallacin Abu hurairah
7.KARATUN MATA NA LITTAFIN ZADIZ ZAUJAINI
Shi ma a masallacin abu hurairah,a kowacce Asabar daga karfe 9:30
na safe zuwa 11:30 na sa fe.

8.KARATUN TAFSIRI
A DUK RANAR LAHADI Asubah zuwa karfe 8:00 na safe.
...........................................................


Shafuka masu Alaka da mu
Basheer journalist sharfadi





Kuna iya tuntu6ar mu ta wadannan hanyoyin
Abdul-majid Ibn Nuh ta face book

KO TA SHAFIN MU NA FALALAR SAHABBAI DAGA BAKIN IMAMAI TA FACE BOOK.

Ko ta watsAp A 07063276717
Bugo mana waya ta nan
Bugo mana waya ta nan
Bugo mana waya ta nan
Ko ta Email A

Home


Copyright © 2014 - 2015By:- Abul-majid Ibn Nuoh Powered by- Basheer journalist sharfadi