Ring ring
Darus-sahaba
1jojlxKOMkX9WyteRe4hGfd...5Tlzwos6Wa8pU99NjJEjmoO7lE72qs...P8zLBUI5VEdw01bf9Bj3WN2UJZQ0kMkumqAOI9CU319yy4DVw
Maraba Da Zuwa Wannan
Shafi Mai Al-barka

wanna shafi yana zuwa muku kai tsaye daga masallacin jumu'a
Jami'u Abu hurairah
Dake kurna y'an kifi titin y'an smogal a karamar hukumar dala dake kano Nigeria
kar kashin jagorancin
Sheik Muhammad Sani Uthman Kurna

Home
Karatut-tukan Sheik Muhammad Thani Uthman Kurna
Mata A Musulunci
Bayanin Zakka
Bayanin Azumi
Bayanin Hajji da Umara
Kasuwanci mai ribar gaske
Muhimmin Sako Zuwa ga Ma'aurata
Tsarin Mu'amala A cikin Musulunci
Hakkokin Manzon Allah s a w Akan Alumarsa
Shin hadin kai zai yiwu tsakanin Ahalussunnah da shi a
Wadanna mata aka Haram tawa musulmi da kuma wanda aka Halarta
Hukunce - Hukunce da suka shafi mata
Jinin Al ada ga mata
Jagoran mai wa azi
Adduo in manzon Allah s a w
Falalar Karatun Al-kur'ani
Falalar Sahabbai {R.A}
Falalar Sahabbai {R.A} Daga bakin Imamai
Tarihi
Falalar Ahlulbait daga bakin Ahlussunnah
Tambayoyi masu muhimmanci A cikin Addinin Musulunci
Ayyukan Zuci
Tattaunawa Ta Nitsuwa
Addinin Shi'a
Hukunce-Hukuncen Da Suka Shafi Mata
Karatut-tukan Malamai da Lakcocin su

2014-10-13

Tags: Abdulmajid

SUWAYE SUKE ZIKIRIN GASKIYA TSAKANIN YAN BIDI,A DA AHLUSSUNA.

SUWAYE NE SUKE HAKIKANIN ZIKIRIN DA YA ZO DAGA QUR'ANI DA SUNNAH, TSAKANIN AHLUSSUNNAH DA AHLUL BIDI'AH??? Sau da dama zakaga cewa 'yan Bidi'ah suna tuhumar Ahlussunnah da cewa Ahlussunnah sun hana ayi zikiri ko kuma kwata-kwatama suce Ahlusuunnah basa yin zikiri. Ya kamata mu danyi bayani a takaice domin mu kare kanmu daga wannan zargin da 'yan Bidi'ah ke yi mana. ¤ FALALAR ZIKIRI. Aya ta farko, Allah madaukakin sarki ya ce: ( فاذكروني أذكركم واشكروا لي ولا تكفرون ) Ma'ana: "Ku ambace ni zan ambace ku, ku gode mini kada ku butulce mini" (Suratul Bakara, aya ta 152) Wannan ayar tana karantar da mu cewa idan muka ambaci Allah (zikiri), to Allah ma zai ambace mu sannan mu gode masa kada mu kasance batulallu. Aya ta 2. ٢. ( يايها الذين ءامنوا اذكروا الله ذكرا كثيرا وسبحوه بكرة واصيلا ) Ma'ana: "Yaa ku wadanda suka yi imani ku ambaci Allah ambato mai yawa" ( Suratul Ahzab, aya ta 41) Wannan ayar tana umurtan dukkanin wani mai imani da cewa su amci Allah ambato mai yawa, ma'ana kuyi zikiri zikiri mai yawa. Sannan kuma abin lura anan shine, ba fa umurni ne ga duk wani musulmi ba, a'a umurni ne da ya takaita ga masu imani. Aya ta 3. ( والذاكرين الله كثيرا والذاكرات أعد الله لهن مغفرة وأجرا عظيما ) Ma'ana: "Da masu ambaton Allah (zikiri) da yawa maza, da masu ambaton sa mata, Allah ya tanadar musu da gafara da lada mai girma" (Suratul Ahzab, aya ta 35) Kai!!! Ashe zikiri babban abune domin kuwa wannan ayar da bada garabasa da rahusa ga masu yin zikiri. Domin kuwa Allah ya tanadar musu da gafara sannan bayan gafarar; Allah zai kara musu da lada, sannan ladanma sai Allah yace "Aziima" Ma'ana lada mai yawa. Ashe zikiri babban abu ne, to amma ya Allah ya ce ayi zikiri??? Sai mu koma suratul A'araf inda Allah madaukakin sarki yake cewa: ٤. ( واذكر ربك في نفسك تضر عا و خيفة ودون الجهر من القول بالغدو والاصال ولا تكن من الغفلين ) Ma'ana: "Kuma ka ambaci Ubangijinka a cikin zuciyarka, kana mai kaskan da kai da tsoro, ba da daukaka murya ba (Tsaka-tsaki tsakanin asirtawa da bayyanawa), da safe da maraice, kuma kada ka zamo daga cikin gafalallu" (Suratul A'araf, aya ta 205). Wannan ayar tace ka ambaci Ubangijinka ma'ana kayi zikiri a cikin zuciyarka. Idan mutum zaiyi zikiri a cikin zuciyarsa baya bukatar ihu da sowa da firgicewa. Sannan sai Allah ya ce kuma a yayin zikirin ka kasance mai kaskan da kai da tsoro a gare shi. Idan ance kankan da kai, ashe kuwa ba za'a sa shauki a cikin zikirin ballentana har a sa ganga da jita da kalangu ko kuma Piano. Kuma Manzon Allah, Annabi Muhammad (SAW) ya ce (Misalin wanda ya ke ambaton Ubangijinsa da wanda ba ya ambaton Ubangijinsa kamar misalin rayayye ne da matacce) Sannan Annabi yace (Shin ba na ba ku labarin mafi alherin ayyukanku ba, kuma mafi tsarkinsu a wajen Sarkin da yake mallakanku, kuma mafi daukakarsu ga darajojinku, kuma mafi alheri gareku daga ciyar da zinariya da azurfa, kuma mafi alheri gare ku da ku hadu da abokan gabanku ku rika dukan wuyayinsu, suna dukan wuyayinku? Suka ce ka ba mu labari Yaa Rasulullah. Sai yace: Ambaton Allah madaukaki) Daga Abbdullahi Ibn Busr, Allah ya yarda da shi, ya ce: ya Ma'aikin! Shari'o'in musulunci sun yi yawa a gare ni, saboda haka ka nuna mini wani abu da zan yi riko da shi. Ya ce: (Kar harshenka ya gushe face yana danye daga ambaton Allah SWT). Kuma Manzon Allah (s.a.w) ya ce (Wanda ya zauna a wani waje bai ambaci Allah a wajen ba, wannan zai zamanto masa abin bibiya a wajen Allah. Wanda ya kwanta a makwanci bai ambaci Allah a wajen ba, shi ma zai zamanto masa abin bibiya a wajen Allah). Abin suna da yawa, amma bara in takaita anan. Duk abinda zakayi, to akwai zikirin da annabi ya karantar matukar dai abin a addini ne ba a cikin hidimomin ra'ayuwa ta duniya ba. Saboda haka ashe mu Ahlussunnah ba wai muna kin zikiri ba ne. Mu abinda mukace ayi zikirin yanda Allah da MansonSa (s.a.w) suka karantar da mu! Kuma hakan mai sauki ne domin akwaisu a rubuce a littatafan Addini. Duk abinda babu Nassi a kansa sannan aka jinginawa Musulunci da wannan abin to ya tabbata a yayi Bidi'ah. Itama kuma Bidi'ah tana cinye ayyukan bawa inji Annabi Muhammad (s.a.w) sannan a hadisin da aka karbo daga wajen Aisha Uwar Muminai (RA) ta ce taji Manzon Allah tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi yace: Duk wanda ya kago wani abunda babu shi a cikin lamarinmu (Na Addini) to an mayar masa) Bukhari da Muslim ne suka ruwaito. Sannan Annabi Muhammad (s.aw) yana tsoratat da mu da yin Bidi'ah a cikin addini kamar yanda yazo a hadisin Abi Najihin al-Irbabu dan Sariyatu (RA) wanda Abu-Dauda da Tirmidhiy suka ruwaito, inda karshen hadisin yake cewa: ( وإياكم و محدثات الأمور' فإن كل محدثة بدعة و كل بدعة ضلالة' وكل ضلالة فى النار ) Yaa Allah ka gafarta mana kurakuren mu. Zan samu lokaci in dan kawo zikirorin da suka tabbata daga Annabi Muhammad (s.a.w) ba irin wanda yan Bidi'ah suke wahalas da kansu a kai ba. " سبحانك اللهم وبحمدك' أشهد أن لا أله إلا أنت' أستغفرك وأتوب إليك " Naku:
Back to posts
Comments:
[2015-07-11 11:17:13] AUWALU MUSA :

YA UBANGIJI ALLAH YA BARMANA IRINKU.

[2016-02-04 16:22:49] Sagiru yusuf abbakar :

Allah yasakawa mall da alkairi amin

[2018-03-06 10:26:04] Loans Online :

pay day online get personal loan installment loans installment loans

[2018-03-17 12:30:40] Getting A Loan :

installment loans no credit installment loans online installment loans installment loans

[2018-03-18 02:38:15] Getting A Loan :

installment loans installment loans guaranteed installment loans installment loans guaranteed

[2018-03-19 23:36:24] Quick Loan :

installment loans for bad credit payday loans lenders only no fuss payday loans no credit

[2018-03-23 22:56:03] Speedy Cash :

installment loans installment loans no credit check installment loans installment loans

[2018-03-28 10:28:03] Online Lenders :

installment loans no credit installment loans installment loans installment loans no credit

UNDER MAINTENANCE

TSARIN LOKUTAN KARATUT-TUKAN MU
TSARA-TSARAN KARATUTTUKAN DA AKE GABATARWA A MAJALISIN DARUS SAHABA,DAKE GOBIRAWA TITIN YAN SUMOGAL.
1.TAHFIZUL QUR'AN.
Daga ranar Asabar zuwa Laraba.
Daga karfe 7:30 na safe zuwa 5:00 na yamma

2.KARATUN MAZA MANYA.
Daga ranar litinin zuwa alhamis, daga karfe 8:00 na dare zuwa karfe 10:00 na dare.
3.KARATUN MATAN AURE.
Ranar alhamis da juma'a daga karfe 2:30 na yamma zuwa 5:00 na yamma.
JERIN KARATUTTUKAN DA SHUGABAN MAJALISIN YAKE GABATARWA A KWANUKAN CIKIN SATI.
1.KARATUN ZAURE
DAGA SAllar asubah zuwa karfe 9:00 na safe a kowacce rana,banda Alhamis da juma'a
2.KARATUN BULUGUL MARARM
A MASAllacin malam bakao dake kurna yan kifi,ranar alhamis magribah zuwa ish'sha
3.KARATUN JAMI'U MUTUNIN TAUHEED WAL AQIDAH.
Ranar lahadi shi ma a masallacin malam bako,magribah zuwa ish'sha.
4.KARATUN MANHAJIL MUSULUM,
MASALLACIN JUMA'A NA ABU HURAIRAH Dake gobirawa yan sumogal,ranar laraba magribah zuwa ish'sha.
5.KARATUN AHKAMUL JANA'IZ
,A MASALLACIN UMAR BIN KATTAB R.A,
Dake dan dinshe kusa da filin dantata,magriba zuwa ish'sha.
Ranar talata

6.KARATUN MATA NA LITTAFIN MANZUMATUL HA'IYYA
A kowacce lahadi daga 9:30 na safe zuwa 11:30 na safe,a masallacin Abu hurairah
7.KARATUN MATA NA LITTAFIN ZADIZ ZAUJAINI
Shi ma a masallacin abu hurairah,a kowacce Asabar daga karfe 9:30
na safe zuwa 11:30 na sa fe.

8.KARATUN TAFSIRI
A DUK RANAR LAHADI Asubah zuwa karfe 8:00 na safe.

Shafuka masu Alaka da mu
Basheer journalist sharfadi

Kuna iya tuntu6ar mu ta wadannan hanyoyin
Abdul-majid Ibn Nuh ta face book

KO TA SHAFIN MU NA FALALAR SAHABBAI DAGA BAKIN IMAMAI TA FACE BOOK.

Ko ta watsAp A 07063276717
Bugo mana waya ta nan
Bugo mana waya ta nan
Bugo mana waya ta nan
Ko ta Email A

Home

Copyright © 2014 - 2015By:- Abul-majid Ibn Nuoh Powered by- Basheer journalist sharfadi